24 Satumba 2014 - 09:57
Shugaba Hassan Rauhani Ya Gana Da Francois Hollande A Birnin New York

Shugaba Hassan Rauhani na jamhuroya musulinci ta Iran ya gada da takwaransa na ksar Kasar Faransa Francois Hollande a birnin New York inda suka halartar babban taron MDD karo na 69 dake gudana a yanlin yanzu.

 Koda yake dai babu wani karin bayani daga shugabanin biyu, aman fadar shugaban kasar faransa tace A ganawar da shuagabnin biyu sukayi a dazu dazunan an ce sun tattauna kan batun kasashen Iraki da Syria musaman kan abunda ya shafi yakin da kasar Amurka da wasu kawayen ta suka kaddamar kan mayakan ISIS dake fafatukar kafa daular Musulunci a yankin gabas ta tsakiya. Sanarwar ta fadar Elisey ta ce shugaba Hollande ya bukaci goyan bayan dukkan masu ruwa da tsaki a gabas ta Tsakiya domin kawo karshen ayukan ta’andaci dake zamen wata babbar barazanan ga zamen lafiya Duniya. A hannu daya kuma an ce shugaba Rauhani da Hollande sun tattauna kan batun makamashin nikiliyar zamen lafiya na kasar Iran da aka jimma ana takaddama kan sa. Marabin dai shugabanin biyu su gana tun bara a yayin irin wanan taro na MDD   ABNA